<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>141</hymn_number>
<title>Ga Duhu Dayawa A Duniyan Nan LW141</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ga duhu dayawa a duniyan nan,
 Zunubi ya kawo duhu.
 Amma hasken darajar Yesu ya zo,
 Ya haskaka zukatanmu.

[V2]
 KORUS
 Haske ya zo a duniyan nan,
 Bari ya shiga zuciyarka
 Dā, cikin duhu na ke, amma
 Na zo wurin hasken Yesu.

[V3]
 2) Ba duhu a wurin Yesu, ko kaɗan,
 Domin shi Mai Gaskiya ne.
 Mu bi cikin haskensa, kusa da shi,
 Zai haskaka zukatanmu.
 Korus

[V4]
 3) Zunubi ya duhunta zuciyarka?
 Ka zo wurin hasken Yesu.
 Ka ba da gaskiya ga Yesu kaɗai,
 Zai haskaka zuciyarka.
 Korus

[V5]
 4) Akwai haske can cikin gidan Allah.
 Ba duhu a cikin Sama,
 Gama Almasihu shi ne haske can
 A cikin gidan daraja.
 Korus</lyrics>
</song>